Amurka ta sanar da shirinta na janye kasashen Afrika ta Kudu da kuma Rwanda daga tsarin nan wanda ya tanbadi saukake kasuwanci tsakanin Washigton da wasu kasashe da ake kira AGOA daga ranar 1 ga Janairu, 2027.
Wakilin harkokin Kasuwanci na Amurka Jamieson Greer ya nuna cewa kasashen biyu ba su cika sharuddan ci gaban wannan gajiyar ba, wanda ya tanadi bai wa wasu kasashe talatin na Afirka damar fitar da dubban kayayyaki zuwa kasuwar Amurka ba tare da haraji ba.
Bayanin ya ci gaba da cewa Shugaba Trump ya yanke shawarar cewa gwamnatocin Rwanda da Afirka ta Kudu sun shiga ayyukan da ba su cika sharuddan cancantar tsarin AGOA ba,” in ji Wakilin Kasuwanci na Amurka Jamieson Greer a cikin wata sanarwa.
Ofishin Jakadancin Amurka a Afirka ta Kudu ya bayyana nadama kan matakin da gwamnatin Amurka ta gabatar.
” Afirka ta Kudu, wacce ita ce babbar mai cin gajiyar shirin, wacce ta mallaki kusan dala biliyan 1.7 a fitar da kayayyaki a karkashin tsarin AGOA a shekarar 2025 kamar ana zarginta da haifar da shinge ga cinikayya da saka hannun jari na Amurka, cin hanci da rashawa, da kuma barazana ga tsaron kasa da manufofin kasashen waje na Amurka.
Washington ta kuma ambaci zaluntar ‘yan Afirka, zargin da Pretoria ta ki amincewa da shi.
Ministan Ciniki na Afirka ta Kudu Parks Tau ya yi korafin cewa yanzu Amurka na tada “sabbin batutuwa” wadanda ba su cikin tattaunawar da aka gudanar tun 2025, duk da karin rangwame da Pretoria ta bayar.
A bangaren Rwanda, Dangantaka ta yi tsami tsawon watanni da dama, inda Washington ta zargi Kigali da bayar da tallafin soja da na kuɗi ga kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo.