Wani babban Jami’in tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa kasar ba zata mika kai ga bukatun kasar Amurka na na mamaye kasar ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto mataimakin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar (SNSC) Ali Bakiri Kani yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar China a birnin Beigin a jiya litinin. Ya kuma kara da cewa ‘Matsayin Tehran wajen kare kasar da kuma bukatun kasar na tsaro da diyauci da kuma kan iyakokin kasar bai sauya ba kuma ba zai taba sauyawa ba.
Kani yace: Iran ba zata taba manta da ta’addancin kasashen Amurka da HKI, wadanda suka farwa kasar da yaki suka kuma kashe jagoran juyin juya halin musulunci kasar Imam Sayyid Aliyul Khjaminaei da iyalansa ba a farkon yakin. Ya ce, wannan laifin ba abinda za’a bari ya ci gaba ko kuma ba tare da daukar fansa ba.
Kani ya kara da cewa yaki a kan kasa wacce take da wayewa irin wannan wanda Amurka ta yi ba zai taba samun nasara ba, kuma sanadiyyar yakin ne al-amuran tattalin arziki a duniya yake fuskantar matsaloli masu tsanani.
Har’ila yau Ali Bakiri Kani ya tattaunawa da shugaban ma’aikatar diblomasiyya na kasar China dangane da yanda za’a kawo karshen yakin da Amurka ta dorawa kasar da kuma hanyoyin dawo da tsaro da kuma zamanlafiya a yankin yammacin Asia.