Ghalibaf : Duk Wani Hari Zai Fuskanci “Martanin Da Ba’a Tsammani”

Muna cikin matakin koli na tsaro, a fannin soja da kuma a fannin aiki inji shi.

Shugaban majalisar dokokin Iran ya yi gargadin cewa duk wani hari daga makiya zai haifar da martanin soja da ba a iya tsammani daga Iran.

Da yake jawabi a lokacin zaman majalisar, Mohammad Bagher Ghalibaf ya jaddada yanayin shirin soja na Iran, yana mai nuni da umarnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei ya bayar kwanan nan ga manyan kwamandoji, wanda ya fayyace girman martanin da ya kamata sojojin su mayar kan duk wani hari da zai iya faruwa kan Iran.

Muna cikin matakin koli na tsaro, a fannin soja da kuma a fannin aiki inji shi.

Idan Washington ta sake yin wani kuskuren lissafi na dabarun yaki, ya kamata ta san cewa a wannan karon za ta fuskanci sabon fagen yaki.

A lokaci guda kuma, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ba da amsa mai karfi da ma’ana ga Amurka, in ji Mista Ghalibaf, yana mai nuni da yanayin da ksar, ta hanyar masu shiga tsakani, ta bayar don sake bude mashigar ruwa ta Hormuz, wadda Tehran ta rufe don ɗaukar fansa kan matakan  Amurka akan kasar.

“Yanzu haka ya ragewa Amurka don guje wa yaki,” in ji shi.

Kallaman nasa dai na zuwa ne a daidai lokacin kasar Amurka ke kara barazanar sake kai hari kan Iran a wani mataki da ta ce na tilastawa Tehran cimma yarjejeniya.

Iran da ta ce a shirye ta ke ta bude mashigar ruwa ta Hormuz a cikin kwanaki biyu muddin Amurka ta amince da sharudanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted