Sabon Jakadan Najeriya A Iran Ya Mika Takardar Kama Aiki Ga Shugaba Pezzekian

Malam Hamza Mohammed Salau, ya bayyana farin cikinsa da ganawa da Dr. Pezzekian, inda kuma ya isar da gaisuwar Shugaban Najeriya ga Iran.

Sabon jakadan Najeriya a Iran, Hamza Muhammad Salau ya mika takardar kama aiki ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian.

A yayin ganawarsu shugaban kasar Iran, ya bayyana karfin dangantakar dake tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Najeriya.

Mista Pezeshkina ya kuma jaddada wajibcin zurfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki, siyasa da al’adu, sannan kuma Iran tana maraba da duk wani shiri na fadada dangantaka da hadin gwiwa da Najeriya.

Shugaban ya bayyana cewa: Muna sa ran Mai Girma Sabon Jakadan na Najeriya zai yi kokari don habaka dangantaka tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki, al’adu da siyasa a lokacin aikinsa.

A nasa bangaren sabon jakadan tarayyar ta Najeriya a Iran Malam Hamza Mohammed Salau, ya bayyana farin cikinsa da ganawa da Dr. Pezzekian inda kuma ya isar da gaisuwar Shugaban Najeriya ga Shugaban kasa da al’ummar Iran, kuma ya nuna ta’aziyya ta gwamnatin Najeriya kan shahadar Jagoran juyin juya halin Musulinci.

Sabon jakadan Najeriya, ya jaddada kudurinsa na karfafawa da zurfafa dangantakar kasashen biyu, ya kuma yi alkawarin a wannan aikisa, zan yi duk mai yiwuwa don inganta matakin dangantaka da cimma burin kasashen biyu.”

Sabon jakadan Najeriya ya kuma lissafa fannonin tattalin arziki, noma, da kiwon lafiya a matsayin fannoni masu mahimmanci a hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, Wadanda ya ce yana burin habaka su tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted