Iran Ta Yi Watsi Da Sabbin Shawarwarin Da Amurka Ta Gabatar

Janar Rezaei ya jaddada cewa mashigin Hormuz ba zai sake kasancewa a bude ba har sai Washington ta cika sharuddan da Tehran ta gindaya.

Jamhuriyar Musulinci Iran ta yi watsi da sabbin shawarwarin da Washington ta gabtaar mata a baya bayan nan.

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran (SNSC), Manjo Janar Mohsen Rezaei, ya yi watsi da sabbin shawarwarin, yana mai bayyana cewa martanin da Amurka ta bayar kan bukatun Tehran na hakika “ba su gamsar ba.”

A cikin wata sanarwa, Janar Rezaei ya jaddada cewa mashigin teku na Hormuz ba zai sake kasancewa a bude ba har sai Washington ta cika sharuddan da Tehran ta gindaya.

“Martanin da Amurka ta mayar kan hakkokin Iran da bukatunta bai gamsar ba, kuma dole ne su amsa sharudda bakwai na Iran gaba daya,” in ji Janar Rezaei.

 “A wannan yanayin ne kawai za a sake buɗe mashigin teku na Hormuz,”inji shi.

Bayannin na Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya zo ne kwanaki kadan bayan da Iran ta tabbatar da cewa ta sake duba wata wasiƙa da Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya aike mata.

An isar da sakon ga Janar Rezaei ta hanyar masu shiga tsakani na Qatar kuma an ruwaito cewa ya gabatar da “tsarin” tattaunawa kai tsaye, inda ake zargin Vance da nuna cewa a sanya shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran a kan teburi tun daga farko – buƙatar da Tehran ta yi ta kin amincewa akai-akai.

 A makon da ya gabata Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar cewa Tehran a halin yanzu ba ta da shirin yin ganawa da jami’an Amurka.

Araghchi ya jaddada cewa shawarar Iran game da sake bude mashigar ruwa ta Hormuz ita ce kawai shirin da za a iya aiwatarwa a yanzu, yana mai lura da cewa masu shiga tsakani na ci gaba da gabatar da shawarwari tsakanin manyan biranen biyu.

Kasar Qatar ta sanar a ranar Talata cewa tana ci gaba “da fatan” za a cimma yarjejeniyar wucin gadi tsakanin kasashen biyu, kuma A halin yanzu suna sake duba ra’ayoyi da shawarwarin da muka gabatar,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Majed Al Ansari ga manema labarai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted