Amurkawa sun fara kada kuri’a a zaben tsakiyar wa’adi na 2026, a wannan Talata.
Koma bayan tattalin arziki da yakin Amurka da Isra’ila suka yi kan Iran da kuma hauhawar farashin rayuwa su ne manyan kalubale ga ‘yan Republican da ke neman ci gaba da rike rinjaye a Majalisar Dokoki.
Zaben na zuwa ne a daidai lokacin da ake bayyana kimar da Shugaban kasar Donald Trump ta ragu.
Ana kallon zaben a matsayin kuri’ar raba gardama kan shugabancin Trump na biyu.
Zaben zai tantance wace jam’iyya ce ke da iko a Majalisar Dokoki ta Amurka a cikin shekaru biyu na karshe na wa’adinsa.
Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa. Dukansu suna taka muhimmiyar rawa wajen zartar da dokoki da sashen zartarwa na Amurka.
A halin yanzu ‘yan Republican suna da iko a majalisun biyu, a daidai lokacin da ‘yan Democrat ske neman samun iko a kan ɗaya ko duka biyun majalisun don takaita ajandar Trump.
Duk da cewa ba ya cikin masu jefa kuri’a, Trump ya sanya kansa a tsakiyar kamfen din.