Venezuela Ta Sake Komawa Mulkin Mallaka Karkashin Trump

Abunda Amurka ta kira yerjeniyar shekaru 100  na hakar danyen man fetur a kasar Venezueala a filayen hakar mai guda 17 wadanda suke dauke da

Abunda Amurka ta kira yerjeniyar shekaru 100  na hakar danyen man fetur a kasar Venezueala a filayen hakar mai guda 17 wadanda suke dauke da ganga kimani biliyon 65 a fili ya tabbatar da cewa mutanen kasar Venezuela sun koma sabon mulkin mallaka.

Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labaran Amurka na bayyana cewa, abinda suka kira yarjeniyar da wani kamfanin hakar man fetur na kasar Amurka wanda ake kira  North American Blue Energy Partiner” ya kulla da gwamnatin kasar  Venezuela ya nuna cewa daga yanzun kuma Amurka ta kwace man fetur na kasar Venezuela har zuwa shekaru 100 masu zuwa, don abinda ya zo cikin yarjeniyar ya nuna cewa gwamnatin kasar Venezuela bata da iko a kan arzikin man fetur na kasar kwatakwata, tunda hatta majalisar da Trump ya kafa na kula da wannan yerjeniyar Amurkawane, kuma kuma a fili sun bayyana cewa manufarta ita ce samarwa Amurka arzikin man fetur na shekaru 100 masu zuwa.

Banda haka a cikin yarjeniyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka tana da cikekken iko a duk yadda yarjeniyar zata gudana.A ranar 3 ga watan Jenerun na wannan shekarar ne sojojin Amurka suka farwa fadar shugaban kasar Venezuela suka sace shugaban da matarsa suka kaisu NewYork.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted