An Ji Karar Tashin Boma Bomai A Tsibirin Keshm Da Bandar Lengeh Na Iran

Wasu kafafen yada labarai a nan kasar Iran sun bada labarin jin fashe-fashe a tsibirin Qeshm da kuma Bandar Lengeh a safiyar yau talata 03-ga

Wasu kafafen yada labarai a nan kasar Iran sun bada labarin jin fashe-fashe a tsibirin Qeshm da kuma Bandar Lengeh a safiyar yau talata 03-ga watan Nuwamban shekara ta 2026 a lardin Hurmuz na kudancin kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran MehrNews ya kara da cewa da farko an ji facewar a tsibirin Qeshm ne sannan daga baya aka ji karar na biyu, a tashar jirage ruwa na Lengeh. Majiyar  dakarun kare juyin juya halin musulunci IRGC a lardin Hurmuzghan ta bayyana cewa, hakan ya faru ne, bayan da suka kakkabo, jiragen yakin Amurka wadanda ake sarrafasu daga nesa kuma samfurin MQN-170 har guda biyu suna ayyukan leken asiri a ruwayen mashigar ruwa ta Hurmuz.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted