Abbas Arakci Ya Mika Wa  Qatar Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Sarkin kasar Hamad Bin Halifah ali-Thani

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon sarkin Qatar Hamad Bin Halifa ali-Thani,tare da bayyana alhini akan hakan. Ministan

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon sarkin Qatar Hamad Bin Halifa ali-Thani,tare da bayyana alhini akan hakan.

Ministan harkokin wajen na Iran ya wallafa sako a shafinsa na X cewa:

” A cikin bakin ciki da alhini,nake mika sakon rasuwar Sheikh Hamad Bin Khalifa ali-Thani.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Ina mika sakon ta’aziyya ga sarki Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Thani da kuma iyalansa na ali-Thani da kuma al’ummar kasar Qatar.”

A karshen sakon, Abbas Arakci ya rubuta cewa: Ina rokon Allah madaukakin sarki da ya yi masa rahama da gafara, ya kuma bayar da hakuri da juriya ga wadanda ya bari.”

Da safiyar yau Lahadi ne dai tashar talabijin din Aljazeera ta watsa labarin rasuwar tsohon sarkin Qatar Hamad Bin Khalifah ali-Thani yana an shekaru 74.

Shi dai Sheikh Hamad Bin Khalifah ali-thani an haife shi ne a 1952,ya kuma fara karatunsa na Firamare a wannan birnin, daga baya kuma ya tafi jami’ar soja ta “Royal Military Academy Sandhurst” a Birniya,sannan daga baya ya yi aikin soja a kasarsa.

Hamad Bin Khalifa ya zama Yarima mai jiran gado 1977 kuma ministan tsaro. Sai dai a 1995 ya yi wa mahaifinsa juyin Mulki a lokacin da ya fita wajen kasar Ziyara. Sai dai a karshe ya sauka daga mukamin nasa a 2013.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted