HKI tana ci gaba da kai wa yankunan Gaza mabanbanta hare-hare da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai a yau Laraba.
Tun da safiyar yau Laraba ne HKI ta kai hari akan wani gida dake unguwar “al-Tuffah” dake cikin birnin Gaza da hakan ya sa mutane 6 su ka yi shahada.
A yankin Jabaliya kuwa jiragen yakin HKI sun kai hari akan wani gida da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3.
A wani labarin kungiyar ” Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba” ta bayyana cewa; Isra’ila ta mayar da yankin Gaza zuwa Makabarta.
Kungiyar ta bayyana cewa; Yadda Isra’ila take fadada wuraren da take kai wa hare-hare ta sama, kasa da ruwa a yankin Gaza , tana korar mazauna yankin ta hanyar amfani da karfi da kuma hana shigar da kayan agaji zuwa yankin.
Kungiyar ta kara da cewa; Abinda Isra’ilan take yi ya sa rayuwa ta yi tsanani a cikin yankin da kuma mayar da shi zuwa babbar makabarta.
Jami’a mai kula da ayyukan kungiyar a Gaza, Amandi Barirol ya bayyana cewa; A halin yanzu Falasinawa ba su da wanda zai taimaka musu.”