Dr. Ali Larijani Ya Gana Da Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Thani

Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani wanda ya isa birnin Doha a dazu da rana, ya gana da sarkin kasar ta Qatar, Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Thani. Tashar talabijin ta “Akhbar” daga nan Iran ta ce, bangarorin biyu sun dauki sa’o’i biyu suna tattaunawa, daga nan kuma babban magatakardar majalisar […]

Iran na bikin shekaru 47 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci

Yau Laraba 11 ga watan Fabarairu, Iran ke bikin cika shekaru 47 da samun nasarar juyin juya halin Musulinci a kasar a karkashin jagoranci mirigayi Imam Khomeini a shekarar 1979. An tsara gudanar da gangamin bikin a birane sama da 1,400 a duk fadin kasar, inda ‘yan jarida na cikin gida da na waje kimanin […]

#Iran47 : Jagora ya yi wa fursunoni 2,108 afuwa

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya amince da yin afuwa wa sama da fursunoni 2,000 a yayin zagayowar cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. A bisa bukatar shugaban sashen shari’a na Iran, matakin ya shafi saki ko sassauci ga hukuncin da ake yanke ga […]

Iran ta sake yin gargadi game da manufofin Isra’ila ga tattauna da Amurka

sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya yi wa Amurka kashedi game da “shishigi da manufofin da Isra’ila ke da su” game da tattaunawar da dake wakana.   Ali Larijani ya yi wa Amurka wannan kashedin ne gabanin ziyarar da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai kai Amurka a wannan Laraba. “Yanzu, Netanyahu yana kan […]

Hezbollah : Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya karfafa ‘yan gwagwarmaya a yankin

babbanSakataren kungiyar Hezbollah ta kasa Lebanon ya ce Juyin Juya Halin Musulunci na Iran a shekarar 1979 ya karfafa kungiyoyin gwagwarmaya a yankin Yammacin Asiya. Sheikh Naim Qassem ya bayyana a wani jawabinsa da aka watsa ta talabijin cewa Juyin Juya Halin Iran ya kasance a matsayin ginshikin goyon baya ga mutanen da aka zalunta […]

Amurka za ta tura sojoji Najeriya domin bada horo

Amurka za ta tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horar da sojoji a yakin da take yi da kungiyoyin dake ikirari da sunan jihadi, kamar yadda jami’ai daga kasashen biyu suka sanar, yayin da Washington ke karfafa hadin gwiwarta da Abuja. Kamfanin dilancin labaren faransa na AFP, ya rawaito Janar Samaila Uba, mai magana da […]