Dr. Ali Larijani Ya Gana Da Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Thani

Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani wanda ya isa birnin Doha a dazu da rana, ya gana da sarkin kasar

Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani wanda ya isa birnin Doha a dazu da rana, ya gana da sarkin kasar ta Qatar, Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Thani.

Tashar talabijin ta “Akhbar” daga nan Iran ta ce, bangarorin biyu sun dauki sa’o’i biyu suna tattaunawa, daga nan kuma babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar ya gana da Fira ministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman  Al Thani Qatar tana a matsayin zango na biyu na ziyarar Dr. Ali Larijani a kasashen yankin tekun Pasha, bayan da a jiya ya kai Ziyara kasar Oman, inda ya gana da sarkinta Haitham bin Tariq Al Said.

Ziyarar Dr. Ali Larijani dai tana a karkashin kokarin Iran na kara bunkasa alaka da kasashen mawabta na yankin tekun Pasha, da kuma tattauna halin da ake ciki a wannan yankin.

A wata hira da ya yi da tashar aljazira ta kasar Qatar, Dr. Larijani ya ce; A Abinda ya faru a Oman shi ne musayar sakwanni, amma Iran ba ta karbi wata shawara yankakkiya daga Amurka ba.

Sai dai kuma ya ce, tattaunawar da Amurka za ta ci gaba.

Haka nan kuma ya yi Ishara da yadda kasashen wannan yankin na yammacin Asiya suke kokarin ganin cewa an sami nasarar a tattaunawar da ake yi.

Bugu da kari Ali Larijani ya ce, batun da ake Magana akansa shi ne na Nukiliya kadai, ba waninsa ba.  Shi ma babu zancen kawo karshen tace sanadarinsa a cikin kasar Iran, domin Iran din tana da bukatuwa da shi domin samar da makamashi da magunguna.

Dangane da yiyuwar yaki kuwa, shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce, Idan har Amurka ta kai wa Iran hari, to kuwa Iran za ta kai wa sansanoninta da suke a cikin wannan yankin hari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted