Netanyahu zai gana da Trump, inda makamai masu linzami na Iran ke kan gaba a cikin ajandar
Fira Ministan Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da cewa: Tattaunawar da zai yi da Shugaban Amurka Donald Trump za ta mayar da hankali ne kan tattaunawa da Iran, yayin da yake neman karfafa matsayin adawar Amurka kan shirin makamai masu linzami na Iran.
Taron ya zo ne bayan tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a Oman kuma shine karo na shida da kasashen biyu suka yi irin wannan ganawa tun bayan komawar Trump Fadar White House.
Taron ya zo ne a daidai lokacin da ake kara samun tashe-tashen hankula a duniya kan ikon Haramtacciyar Kasar Isra’ila a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, amma har yanzu ba a san ko za a tattauna wannan batu a yayin tattaunawar ba.
“A lokacin wannan ziyarar za su tattauna batutuwa da dama: Gaza, yankin, amma ba shakka, da farko tattaunawar da za a yi ne kan batun Iran,” in ji Netanyahu kafin ya tafi Amurka, yana mai cewa, “Zan gabatar wa Shugaban kasar Amurka ra’ayoyinsu kan ka’idojin da ya kamata a gina wadannan shawarwari a kansu.”