babbanSakataren kungiyar Hezbollah ta kasa Lebanon ya ce Juyin Juya Halin Musulunci na Iran a shekarar 1979 ya karfafa kungiyoyin gwagwarmaya a yankin Yammacin Asiya.
Sheikh Naim Qassem ya bayyana a wani jawabinsa da aka watsa ta talabijin cewa Juyin Juya Halin Iran ya kasance a matsayin ginshikin goyon baya ga mutanen da aka zalunta a duk duniya, yayin da ya daga tutar neman ‘yantar da Falasdinu.
Sheikh Qassem ya taya al’ummar Iran murna bikin, yana mai cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya daga Jamhuriyar Musulunci gaban manyan kasashe masu tasiri.
A wani bangare kuma a cikin jawabinsa, Sheikh Qassem ya yi watsi da kokarin da ake yi na kwace makaman Hezbollah da kuma wargaza matsayinta a Lebanon.
Ya kuma ce Isra’ila ta gaza cimma burinta a Gaza, Lebanon, Iran, da Yemen, yana mai dagewa cewa gwamnatin Tel Aviv “ta samu rauni fiye da da”.