Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗi kan matsalar abinci mai tsanani na barazana ga yaran Sudan
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin a ranar Talata cewa: Yara a Sudan na fuskantar matsalar karancin abinci mai tsanani, kuma ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki nan take ba tare da rufe ido kan bala’in jin kai da ke ci gaba da faruwa a kasar ba.
A cewar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya, yunwa ta yadu a jihar Darfur ta Arewa da ke yammacin Sudan, a daidai lokacin da ake ci gaba da rikici tsakanin sojoji da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Rapid Support Forces, wadda ta kashe dubban mutane tare da raba sama da miliyan 11 da muhallansu tun daga watan Afrilun shekara ta 2023.
Kwararru kan harkokin tsaron abinci sun bayyana cewa: Rashin abinci mai gina jiki ya kai matsayin yunwa a wasu yankuna biyu na Arewacin Darfur, Um Buru da Karnoi, yayin da fiye da rabin yaran da ke yankunan arewacin jihar ke fama da rashin abinci mai gina jiki mai tsanani.