sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya yi wa Amurka kashedi game da “shishigi da manufofin da Isra’ila ke da su” game da tattaunawar da dake wakana.
Ali Larijani ya yi wa Amurka wannan kashedin ne gabanin ziyarar da Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai kai Amurka a wannan Laraba.
“Yanzu, Netanyahu yana kan hanyarsa ta zuwa Amurka, Ya kamata Amurkawa su yi tunani, kuma su sa hikima, a game da bukatun Isra’ila game da tattaunawar,” in ji shi.
Larijani ya isa Muscat, babban birnin Oman, a safiyar Talata, kwanaki hudu bayan tattaunawar da Amurka da Iran sukayi game da shirin nukiliyar Iran.
Dama kafin hakan Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi game da bukatun gwamnatin Isra’ila na tunzura Amurka abka wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da yaki a yayin da aka koma tattaunawa tsakanin Tehran da Washington.
Babban jami’in diflomasiyyar ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi da Rasha Today ranar Talata, lokacin da aka tambaye shi game da ziyarar da Netanyahu zai kai Fadar White House, inda ake sa ran ziyarar za ta yi mummunan tasiri ga tsarin diflomasiyya.
Araghchi ya bayyana Netanyahu a matsayin “mai fafatukar kare muradun Isra’ila” wanda “ba ya son” zaman lafiya.
Netanyahu “ba shi da wani buri a zuciyarsa sai yaki” kuma ya yi ta kokarin “jawo Amurka yaki da Iran,” in ji shi.