A gobe Alhamis ne al’ummar Bangladesh za su nufi akwatunan zabe domin kada kur’a a karon farko tun bayan boren da daliban kasar su ka yi, wanda ya kai ga kifar da gwamantin Fira Minista Sheikha Hassina Wajid a 2024.
Da akwai jam’iyyun da dama da suke gasa da juna a cikin zaben da za a yi zuwa gobe.
Da akwai masu kada kuri’a file da miliyan 127, daga cikinsu da kawai wasu miliyan 5 da wannan ne karon farko da za su yi zabe. Adadin mutanen kasar ta Bangaladesh ya kai miliyan 170.
Akan kujerun majalisa 350 da akwai mutane 1981 da suke gogayya da juna a zaben da za a yi. A tsakanin wadannan kujerun 350, an warewa mata kujeru 50.
A tsakanin jam’iyyun da suke yin takara a kasar da akwai na masu kishin musulunci ta “Jama’atul-Islamiyyah al-Bangaliyyah” a karkashin wani kawance na jam’iyyu 11.
A lokacin shugabancin Fira minista Hassinah an haramta wa jam’iyyar ta “Jama’atul-Islamiyyah” shiga cikin harkokin siyasa, sai dai a halin yanzu tana cikin masu tagomashi a tsakanin al’ummar kasar, bayan da aka ba ta damar shiga cikin harkokin zabe.
Wannan shi ne karon farko da mutanen kasar ta Bangladesh mazauna waje za su kada kuri’a,da zummar fadada hanyoyin yin zabe ga mutanen kasar mazauna waje.