Amurka za ta tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horar da sojoji a yakin da take yi da kungiyoyin dake ikirari da sunan jihadi, kamar yadda jami’ai daga kasashen biyu suka sanar, yayin da Washington ke karfafa hadin gwiwarta da Abuja.
Kamfanin dilancin labaren faransa na AFP, ya rawaito Janar Samaila Uba, mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya na cewa “Za mu karbi sojojin Amurka da za su taimaka wajen horarwa da fasaha,” in ji.
Wata mai magana da yawun rundunar sojin Amurka a Afirka ita ma tabbatar da bayanin.
Wannan na zuwa ne yayin da Washington ta shafe tsawon watanni tana matsin lamba kan Abuja game da abinda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin “kisan kare dangi” da ake wa” Kiristoci a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.