Yau Laraba 11 ga watan Fabarairu, Iran ke bikin cika shekaru 47 da samun nasarar juyin juya halin Musulinci a kasar a karkashin jagoranci mirigayi Imam Khomeini a shekarar 1979.
An tsara gudanar da gangamin bikin a birane sama da 1,400 a duk fadin kasar, inda ‘yan jarida na cikin gida da na waje kimanin 7,700 za su gabatar da rahotannin abubuwan dake faruwa.
A Tehran babban birnin kasar dubun dubatar Jama’a ne ke haduwa a dandalin ”Azadi” wato yanci domin nuna goyan bayan su ga tsarin da kasar ke karkashinsa yau shakara 47.
Wadannan tarurrukan suna tunawa da juyin juya halin da al’ummar Iran suka yi wa mulkin kama-karya na ahalin tsohon sarki Shah Pahlavi, da ke da cikakken goyon bayan Amurka a waccen lokacin a 1979.
Imam Khomeini ya dawo daga gudun hijira a ranar 1 ga Fabrairu, 1979, inda ya sami babban tarba daga jama’a makonni bayan da sarki Shah ya bar kasar a tsakiyar watan Janairu.
Gwamnatin Pahlavi ta fadi a rana irin ta yau a 1979, lokacin da sojoji suka juyawa masa baya sukayi mubaya’a ga Juyin Juya Halin.
Bukin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke kara matsin lamba ta hanyar kakaba tsauraran takunkumai da kuma barazanar soji kan Iran.
Haka zalika bukin na wannan karo ya zo ne a kasa da wata guda da zanga zangar tsadar rayuwa da akayi a kasar wacce ta rikide zuwa tarzoma sakamakon tsoma baki na wasu kasashen ketare musamman Amurka da Isra’ila da kuma wasu na yamma da suka ingiza masu zanga zangar.
Kafofin yada labarai na Iran, sun ce bata-gari da ‘yan ta’adda dake samun goyan baya daga ketare sun amfani da damar wajen wajen kutse tare da hadassa barna da kisna jama’a a yayin zanga zangar.
Jimillar mutane 3,117 ne suka rasa rayukansu a lokacin zanga-zangar.
Hukumonin Iran sun ce duk da juyayin da ake ciki na wadanda suka rasa rayukansu, za’a nunawa duniya hadin kan ‘yan kasar kamar a yayin yakin kwanaki 12 da kasar ta fuskanta a watan Yunin shekarar da ta shude..