Senegal: Wani Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa Sanadiyyar Taho Mu Gama Da Jami’an Tsaro

Mahukunta a kasar ta Senegal sun ce dalibin mai suna Abdullahi Bah, ya rasa ransa bayan zubar jini daga kansa da ya ji ciwo, kuma

Mahukunta a kasar ta Senegal sun ce dalibin mai suna Abdullahi Bah, ya rasa ransa bayan zubar jini daga kansa da ya ji ciwo, kuma tuni an bude bincike akan lamarin.

Shi dai dalibin yana karatun tiyatar hakori ne, a shekara ta biyu a jami’ar Sehikh Anta Diop a birnin Dakar.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya watsa wani faifen bidiyo dake nuna dalibai suna dirowa daga tagogin ginin jami’ar bayan da gobara ta tashi a cikinsu.

Tun a cikin watan Disamba da ya wuce ne daliban jami’an Shekin Anta-Diop na kasar Senegal suke Zanga-zanga akan neman gwmnatin kasar ta ci gba da daukar nauyin yin karatunsu, wanda ya kai su ga yin taho mu gama da jami’an tsaro.

A  ranar juma’ar da ta  gabata ne aka fara samun hargitsin a cikin jami’ar, kuma wasu Karin jami’o’in kasar sun bi sahun yin Zanga-zanga.

Wani dalibi na jami’ar Sheikh Anta-Diop ya fada wa manema labaru cewa, rabon da a biya su kudin taimakon da gwamnati take ba su, an dauki watanni 13, don haka ba za su iya ci gaba da jurewa halin da ake ciki ba.

A farkon watan Disamba na 2025 ne dai daliban jami’a su ka hau kan titunan suna yin Zanga-zanga saboda jinkirin biyansu hakkokinsu na lokaci mai tsawo.

Daliban sun rika jefawa ‘yan sanda duwatsu, yayin da su kuma su ka rika watsa musu hayaki ma isa hawaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted