Al’ummar Iran Sun Gudanar Da Manyan Taruka Domin Tunawa Da Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci

An gudanar da manyan gangami a fadin Iran na tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci An fara tattakin tunawa da zagayowar ranar samun

An gudanar da manyan gangami a fadin Iran na tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci

An fara tattakin tunawa da zagayowar ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a babban birnin Tehran, da kuma dukkan lardunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

An gudanar da tattakin a biranen Iran daban-daban domin tunawa da cika shekaru 47 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci, tare da halartar jama’a daga ko’ina cikin kasar.

Tun daga wayewar garin yau Laraba, miliyoyin mutane sun yi tururuwa zuwa titin “Inqilabul -Islami” cikin tattakin farin ciki, suna daga tutoci da kuma rera take, daga karshe suka isa dandalin Azadi, wurin da ake gudanar da manyan taruka da ake gudanar da murnar zagayowar muhimman ranaku.

A ranar Litinin, Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Seyyed Ali Khamenei, a cikin wani sako da ya aika wa al’ummar kasar ta gidan talabijin a jajibirin cikan shekaru 47 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma “Ranar Allah” (11 ga Fabrairu), ya yi kira ga al’ummar Iran da su sanya yanke kauna a zukatan makiya ta hanyar shiga cikin tattakin ranar 11 ga Fabrairu, ranar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted