Iran Ta Gargadi Hukumar IAEA Kan Barazanar Trump Kan Cibiyoyin Nukliyarta

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da kuma kuma sauran cibiyoyin kasa da kasa a Geneva ya gargadi hukuma mai kula da makamashin nukliya ta duniya wato IAEA kan cewa barazanar da shugaban kasar Amurka yakewa cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran, barazana ce ga hukumar kanta. Saboda idan Amurka zata yi gabanta ta yi […]
Shekara Ta 2026 A Tehran: Kirstoci Sun Gudanara Da Bukukuwan Shigowar Sabuwar Shekara A Iran

A dai dai tsakiyar daren jiya ne aka fara bukukuwan shigar sabuwar shekara ta 2026 a nan Tehran da kuma garuruwan da kiristoci suke zama a duk fadin Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shirin da aka gudanar a cocin Targ-manchat da kan titin Wahidi a dai dai shigowar sabon […]
An Gudanar da Bukukuwan Shigowar Sabuwar Shekarar Ta 2026 A Kasashen Duniya Da Dama

An gudanar da bukukuwan shigowar sabuwar shekara a kasashen duniya daban daban daga ciki har da kasar China wacce take daga cikin kasashen duniya wadanda shekarar take fara shigowa ta wajensu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an yi wasan wuta da kuma kide-kide da raye-raye da wakoki da dama a […]
Siriya: An Kashe Jami’in Tsaro Guda, Wasu 2 Suka Ji Raunin A harin Kunan Bakin Wake A birnin Halab

A kasar Siriya kuma jami’in tsaro guda ne ya rasa ransa a wani coci a birnin Halan na arewacin kasar, sannan wasu abokan aikinsa biyu suka ji rauni, a lokacinda suka tsaida wani dan ta’adda suna kuma bincikensa, sai ya tada damarar boma boman da ya nade a jikinsa. Shafin yanar gizo na labarai Arab […]
Kungiyar Daliban Jami’o’i A Najeriya Ta Kasa “NANS” Ta Bukaci A Fito Don Nuna Kin Sabuwar Dokar Haraji

Kungiyar daliban Jami’o’ii a tarayyar Najeriya ‘NANS” ta fara kira ga daliban jami’o’ii da sauran yan kasa da su fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da sabuwar dokar haraji wanda yakamata ya fara aiki a yau Alhamis daya ga watan Jenerun shekara ta 2026. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu […]
AFCON 2025: Jerin kasashen da zasu fafata a rukunin ‘yan 16

A gasar cin kofin kwallon kafa da kasar Morocco ke karbar bakunci, an fitar da sunayen kasashen da suka yi nasarar zuwa rukunin ‘yan 16. Kasashen sun hada da Mali, Morocco, Afrika ta Kudu, Masar, Najeriya da Aljeriya, Senegal, Tanzania, Benin da DRC, Ivory Coast, Burkina Faso, Tunusia, Sudan, Kamaru da Mozambique. Za a fara […]
Nijar ta kaddamar da aikin rubuta Tarihinta da kanta

Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani aiki na ƙasa na musamman don rubuta gabadayen tarihinta da kanta. An kafa wani kwamiti na musamman a Yamai a hukumance don tattarawa, yin nazari, da tsarawa, da rubuce-rubucen tarihin mai kyau. A cewar Firaministan Nijar Mahamad Lamine Zein, wannan shiri yana da nufin samar wa ‘yan Nijar fahimta […]
Iran ta aike wa IAEA wasika game da barazanar Amurka

Iran ta aika wa babban daraktan Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya wasika, tana mai yi masa gargadi game da mummunar barazanar Amurka ta baya bayan nan. Iran ta ce barazanar ta Amurka kan cibiyoyin nukiliyarta barazana ce ga sahihancin hukumar IAEA da yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta duniya. Dangane da barazanar da […]
(UNRWA): Takunkuman Isra’ila kan kungiyoyi agaji nakaso ne ayyukan jin

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta bayyana sabbin takunkuman da Isra’ila ta sanya wa kungiyoyin agaji na duniya da masu zaman kansu zasu kara gurgunta ayyukan jin kai a yankin Gaza da aka killace. Shugaban hukumar Philippe Lazzarini ya yi gargadin cewa sabbin takunkuman suna iya haifar da rugujewar ayyukan agaji […]
Tehran ta yi Allah wadai da CNN kan maimaita “Tatsuniyar” Netanyahu

Gwamnatin Iran ta yi Allah wadai da wani rahoton tashar talabijin ta CNN, wanda ta ce ya maimaita ”Tatsuniyar” da Isra’ila ta jima tana yi. A cikin wani sako da aka wallafa kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya yi tir da bidiyon da tashar labarai ta Amurka CNN ta hada, wanda ya nuna […]
IRIGC: Sun Aike Da sakon Ta’aziyar shahadar Abu Obeida

Dakarun karun juyin musulunci na kasar iran IRIGC ta aike da ta’aziyar shahadar Abu obeida kakakin kungiyar izzuden qassam, kuma ta bayyana kisan gillar da Isra’ila ta yi masa a matsayin wata alama ta samun nasarar kungiyoyin gwagwarmayar falasdinu, da kuma kashe guiwar sojojin isra’ila, kuma makoma tana hannun yan gwagwarmaya. A cikin bayanai da […]
MDD : Takunkumin Isra’ila Ya Haifar Da Babban Hatsari Da Kara Tsananta Rikici A Gaza

Shugabanar hukumar bada agaji a yankin na gaza UNRWA yayi gargadin cewa sabon matakin da Isra’ila ta dauka kan kungiyoyin bada a gaji na kasa da kasa sun kara gurgunta ayyukan jin kai a yankin Gaza, yace mataken suna da hatsari sosai kuma sun kara kosantowar rugujewar ayyukan gaji a yankin na Gaza. Wannan sanarwar […]
Gwamnatin Nijeriya Ba Za Ta Cire Kuɗi Kai-Tsaye Daga Asusun Bankin Mutane Ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa sabbin dokokin haraji da za su fara aiki a yau 1 ga watan Janairu, 2026, ba za su hada da cire kudi kai-tsaye daga asusun banki na mutane ba. Shugaban Kwamitin Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce mutane za […]
Iran Ta yi Kira Da’a Dauki Mataki A Yankin Domin Kare Hadin Kan Kasar Yamen

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya nuna damuwarsa matuka game da yadda alamura ke kara dagulewa a kudanci da gabashin kasar yamen , don haka yayi kira ga masu fada aji a yankin da su dauki matakin hadin kan kasar da martabar kasar ta larabawa. Araqchi yayi wannan kiran ne a wata tattaunawa […]
Kasar Rasha Tayi Gargadi Bayan Da Trump Yayi Barazanar Yi Yuwar Kai Wa Iran Hari

Fadar kremlin ta kasar rasha tayi gargadi da ayi taka tsan-tsan kuma ta kira dukkan bangarori da su guji abin da zai tada hankali a yankin, bayan da shugaban Amurka Donald Trump yace Washington za ta iya goyon bayan kai wa kasar iran wani hari, idan ta ci gaba da kera muggan makamai. Kiran da […]
IRIB Sahab Network: Sauyi daga tsohuwar hanyar sadarwa zuwa cibiyar labarai ta duniya

Pars Today – A cikin duniyar da samun ƙarin tashoshin watsa shirye-shirye ba su daidaita da ƙarfin kafofin watsa labarai mafi girma ba, Cibiyar Sahab ta IRIB ta fara sabuwar hanyar tasirin ƙasashen duniya ta hanyar canzawa zuwa cibiyar watsa labarai ta hanyar labarai. A cikin ‘yan shekarun nan, babban tambayar game da makomar kafofin […]