Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya nuna damuwarsa matuka game da yadda alamura ke kara dagulewa a kudanci da gabashin kasar yamen , don haka yayi kira ga masu fada aji a yankin da su dauki matakin hadin kan kasar da martabar kasar ta larabawa.
Araqchi yayi wannan kiran ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi tsakaninsa da ministan harkokin kasar Baharain Abdullatif bin rashid al zayani inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma irin ci gaban da aka samu a yankin.
A lokacin tattaunawar tasu ministan iran yace babbar mafita game da rikicin kasar Yamen shi ne komawa teburin tattaunawa da zai kunshi dukkan bangarorin kasar yamen, yace iran a shirye take ta kasance bangaren tattaunawar don ganin an warware rikicin da zai shafi dukkan bangarorin kasar. Anasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Bahrain ya jaddada game da muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar Yamen da ma yankin baki daya, kuma dukkan ministocin sun nuna fatansu ganin cewa kokarin diplomasiyar da ake yi zai kai ga waraware matsalar.