Kasar Rasha Tayi Gargadi Bayan Da Trump Yayi Barazanar Yi Yuwar Kai Wa Iran Hari

Fadar kremlin ta kasar rasha tayi gargadi da ayi taka tsan-tsan kuma ta kira dukkan bangarori da su guji abin da zai tada hankali a

Fadar kremlin ta kasar rasha tayi gargadi da ayi taka tsan-tsan kuma ta kira dukkan bangarori da su guji abin da zai tada hankali a yankin, bayan da shugaban Amurka Donald Trump yace Washington za ta iya goyon bayan kai wa kasar iran wani hari, idan ta ci gaba da kera muggan makamai.

Kiran da kasar rasha ta yi na yin taka tsan-tsan ya nuna irin sassaucin da take samu yayin da take ci gaba da karfafa dangantakarta da kasar iran kuma tana duba yanayin na siyasa mai sarkakiya musamman bayan yakin da take yi da kasar Ukrain.

A ranar litinin ne Trump tare da fira ministan israi’la banjamin Natanyaho yayi gargadin cewa iran na  kokari wajen sake dawo da shirinta na nukiliya bayan harin da Amurka takai a watan yulin shekarar da ta gabata, duk da cewa Tehran ta sha nanatawa cewa shirinta na makamashin nukiliya ne na zaman lafiya, Sai dai kasar rasha da ta kara karfafa dangantakarta da kasar iran a yan shekarun nan tana kokarin hana afkuwar dok wani tashin hankali a yankin wanda zai iya yin karan tsaye ga dangantakarta ta kasa da kasa, don haka ta ce ya zama wajibi a dakatar da duk wani mataki da zai iya sake jefa yankin cikin tashin hankali.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted