Shugabanar hukumar bada agaji a yankin na gaza UNRWA yayi gargadin cewa sabon matakin da Isra’ila ta dauka kan kungiyoyin bada a gaji na kasa da kasa sun kara gurgunta ayyukan jin kai a yankin Gaza, yace mataken suna da hatsari sosai kuma sun kara kosantowar rugujewar ayyukan gaji a yankin na Gaza.
Wannan sanarwar tana zuwa ne bayan da wani dan majalisa ya bada izini ga gwamnati ta yanke wuta da ruwa da man fetur da kuma hanyoyin sadarwa na hukumar bada agaji ta UNRWA kuma ya bada damar kwace kadarorin majalisar dinkin duniya a gabashin birnin Kudus da aka mamaye da kuma hedikwatar hukumar da kuma babbar cibiyar koyar da sanao’i
Isra’I’la ta hana kungiyoyin agaji guda 37 na kasa da kasa aiwatar da ayyukan agaji a yankin na Gaza ciki har da kungiyar likitoci da basu da shamaki, da kungiyar yaki da yunwa da kuma kungiyar oxfarm da kuma kungiyar kula da yan gudun hijira da dai sauransu.
Isra’ila ta hana hukumar UNRWA aiki a yankunan da ta mamaye bayan da ta zargi wasu daga cikin ma’aikatanta da hannu a harin da aka kai mata na dufanul Aqsa a watan oktoban shekara ta 2023, sai dai duk bukatar da ta gabatarwa da isra’ila na nuna hujjojin dake tabbatar da zargin amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa.