Kungiyar daliban Jami’o’ii a tarayyar Najeriya ‘NANS” ta fara kira ga daliban jami’o’ii da sauran yan kasa da su fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da sabuwar dokar haraji wanda yakamata ya fara aiki a yau Alhamis daya ga watan Jenerun shekara ta 2026.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana fadar cewa babu abu da zai hana fara aiwatar da shirin harajin ba a ranar Talatan da ta gabata.
Shugaban ya bayyana haka ne a dai dai lokacinda mutane da kungiyoyi da dama suke kiran shugaban da ya dakatar da aiwatar da wannan shirin sabon haraji saboda rudun da ke cikinsa, da kuma yiyuwar cutar da yan Najeriya da dama.
Banda haka akwai zargin cewa dokar harajin wanda majalisar dokokin kasar ta amince da ita ba itace, gwamnatin shugaba Tinubu take son aiwatar da ita ba, saboda an sauya wasu al-amura a cikinta bayan da majalisar dokoki ta amince da ita.
Kafin haka dai, kungiyar lawyoyi ta kasa (NBA),, da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da kuma, kungiyar marasa rinjaye a majalisar dokokin kasa duk sun bukaci shugaban ya dakatar da aiwatar da wannan dokar ta haraji har zuwa lokacinda za’a warware takaddamar da ake yi dangane da ita.