(UNRWA): Takunkuman Isra’ila kan kungiyoyi agaji nakaso ne ayyukan jin

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta bayyana sabbin takunkuman da Isra’ila ta sanya wa kungiyoyin agaji na duniya da masu zaman

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya kan ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta bayyana sabbin takunkuman da Isra’ila ta sanya wa kungiyoyin agaji na duniya da masu zaman kansu zasu kara gurgunta ayyukan jin kai a yankin Gaza da aka killace.

Shugaban hukumar Philippe Lazzarini ya yi gargadin cewa sabbin takunkuman suna iya haifar da rugujewar ayyukan agaji a Gaza.

“Sabbin takunkuman abun damuwa ne sannan sun sabawa dokar jin kai ta duniya da kuma kara toshe ayyukan agaji,” in ji shugaban UNRWA.

Wadannan kalamai sun zo ne bayan da Isra’ila ta zartar da wata doka da ta ba wa jami’an gwamnati izinin katse ruwa, wutar lantarki, mai, da hanyoyin sadarwa zuwa wuraren UNRWA da kuma ba da damar kwace kadarorin Majalisar Dinkin Duniya a Gabashin Kudus da aka mamaye, gami da hedikwatar hukumar da kuma babbar cibiyar horar da sana’o’i.

A cikin sakonsa, Lazzarini ya kuma yi kira ga al’ummar duniya da su nuna adawa da kokarin Isra’ila na takaita ayyukan kungiyoyin agaji na duniya da na agaji.

Isra’ila dai ta haramta kungiyoyin jin kai na duniya 37 aiki a Gaza, ciki har da manyan kungiyoyi kamar Doctors Without Borders (MSF), CARE, Action Against Hunger, rassan Oxfam, Norwegian Refugee Council, World Vision, da Caritas.

A ranar Laraba, kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da matakin na Isra’ila na soke lasisin kungiyoyin agaji na duniya” da ke aiki a Gaza da Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted