Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa sabbin dokokin haraji da za su fara aiki a yau 1 ga watan Janairu, 2026, ba za su hada da cire kudi kai-tsaye daga asusun banki na mutane ba.
Shugaban Kwamitin Haraji na Fadar Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce mutane za su bayyana kudin shigarsu da kansu sannan su biya haraji a inda ya dace. Ya bayyana cewa tsarin yana da sauki, bayyananne, kuma ba zai wahalar da talakawa ba.
Oyedele ya kara da cewa masu kananan sana’o’i da wadanda ke da karamin albashi za su fi amfana, saboda dokokin sun tanadi kariya ga masu rauni kuma sun tabbatar da adalci a biyan harajin.
Shugaba Bola Tinubu ma ya tabbatar da cewa za a aiwatar da sabbin dokokin haraji kamar yadda aka tsara, duk da sun fuskanci suka daga wasu kugiyoyi.
Gwamnati ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su goyi bayan dokokin, tana mai jaddada cewa za su rage nauyin haraji, kare masu karamin albashi, da kuma bunkasa tsarin haraji na adalci.