Nijar ta kaddamar da aikin rubuta Tarihinta da kanta

Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani aiki na ƙasa na musamman don rubuta gabadayen tarihinta da kanta. An kafa wani kwamiti na musamman a Yamai

Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani aiki na ƙasa na musamman don rubuta gabadayen tarihinta da kanta.

An kafa wani kwamiti na musamman a Yamai a hukumance don tattarawa, yin nazari, da tsarawa, da rubuce-rubucen tarihin mai kyau.

A cewar Firaministan Nijar Mahamad Lamine Zein, wannan shiri yana da nufin samar wa ‘yan Nijar fahimta mai kyau ta tarihin kasar da aka tsara game da abubuwan da suka gabata.

Ya jaddada cewa koyar da tarihi yana taka muhimmiyar rawa wajen fahimtar gadonmu da kuma ƙarfafa fahimtar haɗin kan ƙasa.

Ya tabbatar da cewa sanin wannan yana taimakawa wajen habaka ci gaban kasa mai hangen nesa.

An dorawa kwamitin alhakin tattara bayanai cikin sauri daga dattawa, masu binciken tarihi.

A cewar Ali Mahaman Lamine Zeine, dole ne a tuntuɓi hukumomin gargajiya, shugabannin addinai, da masu fasaha don samar da labarin tarihi mai haɗin kai wanda ke nuna gaskiyar rayuwa.

Tun bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a Nijar ne, sabbin mahukunatan kasar suka raba gari da faransa wacce ta yi wa kasar mulkin mallaka kuma tun lokacin ne kasar ke kokarin ta shafe duk wani abu mai alaka da ‘yan mulkin mallaka musamman faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted