Iran ta aike wa IAEA wasika game da barazanar Amurka

Iran ta aika wa babban daraktan Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya wasika, tana mai yi masa gargadi game da mummunar barazanar Amurka ta

Iran ta aika wa babban daraktan Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya wasika, tana mai yi masa gargadi game da mummunar barazanar Amurka ta baya bayan nan.

Iran ta ce barazanar ta Amurka kan cibiyoyin nukiliyarta barazana ce ga sahihancin hukumar IAEA da yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta duniya.

Dangane da barazanar da Amurka ta yi kwanan nan kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran, Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Ƙungiyoyin Kasa da Kasa da ke Vienna ya aike wa Rafael Grossi, ya yi masa gargadi game da mummunan sakamakon wannan barazanar ta Amurka.

A cewar Iran “Dole ne a yi Allah wadai da irin wannan.

An buga wannan sakon ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya sake nanata kalamansa da barazanar da ya yi a baya kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ganawarsa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted