A gasar cin kofin kwallon kafa da kasar Morocco ke karbar bakunci, an fitar da sunayen kasashen da suka yi nasarar zuwa rukunin ‘yan 16.
Kasashen sun hada da Mali, Morocco, Afrika ta Kudu, Masar, Najeriya da Aljeriya, Senegal, Tanzania, Benin da DRC, Ivory Coast, Burkina Faso, Tunusia, Sudan, Kamaru da Mozambique.
Za a fara zagayen na ‘yan 16 na gasar AFCON ta 2025 a ranar Asabar, 3 ga Janairu a Tangier tare da Senegal da Sudan kuma za a kammala a ranar Lahadi, 6 ga Janairu da fafatawa tsakanin Algeria da DR Congo a Rabat.
Wassanin da asu dauki hankali sun hada da Mali da Tunisia sai Morocco mai masaukin baki da Tanzania.
Kamaru kuwa zata kece raini da Afirka ta Kudu, sai na Ivory Coast da za karawa da Burkina Faso.
Wasan Aljeriya da DR Congo zai gudana a ranar 6 ga Janairu a Rabat, a filin wasa na Moulay El Hassan.
Wannan zai zama karo na uku da Aljeriya za ta fafatawa tsakaninta DR.Congo a tarihin gasar AFCON.