Tehran ta yi Allah wadai da CNN kan maimaita “Tatsuniyar” Netanyahu

Gwamnatin Iran ta yi Allah wadai da wani rahoton tashar talabijin ta CNN, wanda ta ce ya maimaita ”Tatsuniyar” da Isra’ila ta jima tana yi.

Gwamnatin Iran ta yi Allah wadai da wani rahoton tashar talabijin ta CNN, wanda ta ce ya maimaita ”Tatsuniyar” da Isra’ila ta jima tana yi.

A cikin wani sako da aka wallafa kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya yi tir da bidiyon da tashar labarai ta Amurka CNN ta hada, wanda ya nuna ikirarin ”karyar” da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da shirin nukiliyar Iran.

“Wannan karya ce da farfaganda, inji kakakin ma’aikatar harklokin wajen Iran din.

Wannan bidiyon na CNN ya tattara ikirarin ‘karya na shekaru talatin da Netanyahu ya yi game da shirin nukiliyar Iran, inda yake gargadin cewa Iran na gab da mallakar bam din nukiliya.

Bidiyon, wanda aka watsa a CNN a ranar Talata, 30 ga Disamban da mukayi ban kwana da shi, ya yi daidai da zarge-zargen da Netanyahu ya yi marasa tushe tun 1996 game da ayyukan nukiliyar Iran, yana nuna Tehran a matsayin “barazana da ke gabatowa.”

Fitowar bidiyon ta zo ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maganganu masu tayar da hankali a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Netanyahu.

Ya yi barazanar daukar matakin soja, yana gargadin cewa Amurka za ta kai hari kan makamai masu linzami na ballistic na Iran da cibiyoyin nukiliya idan Tehran ta yi yunkurin sake gina su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted