Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire

Kasar Cote De Voire ta sanar da tsaurara harkokin tsaro akan iyakokinta na Arewa domin fuskantar ‘yan hijira da suke kwararowa daga kasar Mali da take fama da rikicin masu dauke da makamai. Majalisar tsaron kasar “Cote De Voire” ce ta bai wa sojojin kasar umarni da su tabbatar da tsaro a kan iyakoki, kamar […]

 Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza

 Hukumar Agaji mai kula da Falasdinu dake karkashin MDD, ( Unrwa)  da ta fitar da wannan alkaluman na yawan gidajen da ‘yan mamaya su ka rushe, ta kuma kara da cewa; Da akwai dubban iyalai Falasdinawa da suke raywua a cikin hemomi kuma a cikin mawuyancin yanayi, ga shi kuma sanyi yana karatowa. Hukumar ta […]

Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi kira ga jami’an diplomasiyyar kasar Iran da su kai karar shugaban kasar Amurka Donald Trump a kotunan kasa da kasa, bayan da ya yi  furuci da cewa shi ne ya jagroanci harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kawo wa Iran. Ayatullah Sayyid […]

Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya

Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take samar da tan miliyan 1.5 a kowace shekara. Bayannin ya zayyana Kasashe goma mafiya samar da dabino a duniya wadanda su ne Masar, Saudiyya, Iran, Aljeriya, Pakistan, Iraki, Sudan, Hadaddiyar […]

Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza

Rasha, China, da wasu kasashen Larabawa da dama sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yaki da kuma rashin wani muhimmin matsayi ga Hukumar Falasdinu bayan yakin Gaza da aka gabatar a daftarin kudirin shirin tsagaita wuta na Shugaba Donald Trump na Amurka. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar kasashen sun yarda cewa tattaunawa ta […]

Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya

Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. Duk da shakkun da Amurka ta yi, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsawaita wa’adin aikin tawagar ta MINUSCA, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa ranar 15 ga […]

Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya a yankin

Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin […]

Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka

Tehran ta yi Allah wadai da sanarwar da kasashen gungun G7 suka fitar kwanan nan, wadda ta amince da matakan da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana zarge-zargen […]

Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu

Iran da China sun bayyana shirinsu na haɓaka alaƙar da ke tsakaninsu da kuma haɓaka haɗin gwiwa bisa ga yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu. Jakadan Iran a China Abdolreza Rahmani Fazli ya ce a ranar Alhamis cewa Tehran a shirye take ta ƙarfafa cikakken haɗin gwiwa da Beijing a sassa daban-daban a matsayin […]

Abdoulaye Diop: ‘Yan Tawaye Ba Za Su Iya Mamaye Dukkan Kasar Mali Ba

Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya yi watsi da ra’ayin cewa kungiyoyi masu dauke da makamai za su kwace babban birnin nan ba da jimawa ba, yana mai cewa “ba za a iya tunanin hakan ba.” A ranar Lahadi ne Tarayyar Afirka ta yi kira da a dauki matakin gaggawa na kasa da kasa […]

Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg

Shugaban Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya soki Shugaban Amurka Donald Trump saboda kin halartar taron shugabannin G20 da ke tafe, yana mai gargadin cewa yunkurin ware kasar da ke karbar bakuncin taron ba zai yi wani tasiri ba ga taron ko sakamakonsa. Trump ya sanar da cewa shi ko wani jami’in Amurka ba za […]

MDD ta nuna damuwa game da rahotannin kisan gilla a El Fasher

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “damuwarsa mai zurfi” game da rahotannin “mummunan kisan gillar da kuma take hakkin bil’adama masu tsanani a El Fasher,” Sudan, yana mai cewa “tashin hankali ma yana karuwa a Kordofan.” A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X a ranar Alhamis, Guterres ya jaddada bukatar […]