Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka

Tehran ta yi Allah wadai da sanarwar da kasashen gungun G7 suka fitar kwanan nan, wadda ta amince da matakan da Amurka da Tarayyar Turai

Tehran ta yi Allah wadai da sanarwar da kasashen gungun G7 suka fitar kwanan nan, wadda ta amince da matakan da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana zarge-zargen kin jinin Iran dake kunshe a cikin sanarwar karshe ta gungun kasashen da suka hada da (Faransa, Amurka, Kanada, Japan, Burtaniya, Italiya, da Jamus), a matsayin “marar tushe, kana mai cike da karairayi.”

Baghhai ya yi ikirarin cewa yunkurin Amurka da Tarayyar Turai na mayar da takunkumin kai tsaye daidai yake da amincewa da wani laifi na kasa da kasa.

Da yake sukar kasashen kungiyar G7 kan yin kira ga Iran da ta ci gaba da hadin gwiwa da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Mr. Baghai ya jaddada gazawarsu wajen hana hare-haren Isra’ila da Amurka kan cibiyoyin nukiliya na zaman lafiya a Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments