Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi kira ga jami’an diplomasiyyar kasar Iran da su kai karar shugaban kasar Amurka Donald Trump a kotunan kasa da kasa, bayan da ya yi furuci da cewa shi ne ya jagroanci harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kawo wa Iran.
Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma kara da cewa, ya kamata a fitar da bayani na yin tir da wannan maganar sannan kuma a kai kara a cibiyoyin duniya.
Da ya koma yin Magana akan hijabi kuwa, limamin na Tehran ya bayyana cewa, sanya hijabi ga mata,hukunici ne da addini da kuma doka, sannan ya ambato wani marubuci dan Amurka da yake cewa: Idan har matan Iran su ka cire suturar hijibi to sun fada cikin tarkon makarkashiyar kungiyar leken asirin Amurka ( C.I.A) wacce ke nufin kifar da tsarin musulunci da rusa Iran.
Limamin ya kuma yi kira ga matan da su sake tunani akan kare addininu da kuma kasarsu, wadanda ba su sanya suturar hijabi su sauya tunani.