Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya

Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take

Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take samar da tan miliyan 1.5 a kowace shekara.

Bayannin ya zayyana Kasashe goma mafiya samar da dabino a duniya wadanda su ne Masar, Saudiyya, Iran, Aljeriya, Pakistan, Iraki, Sudan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman, da Tunisiya, wanda ya nuna Iran na cikin kasashe na uku na farko.

Kuma a yadda Iran ke fitar da tan 430,000 na dabino a kowace shekara, hakan ya sa ta kasance ta farko wajen fitar da dabino a duniya, sai Saudiyya da tan 390,000 sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da tan 330,000.

Fitar da dabino daga Iran an kiyasta yana samar mata da kimanin dala miliyan 430, a nau’in dabino iri bakwai dake akwai a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments