Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya

Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Duk da shakkun da Amurka ta yi, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsawaita wa’adin aikin tawagar ta MINUSCA, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa ranar 15 ga Nuwamba, 2026.

Duk da haka, Majalisar ta nuna yiwuwar rage wa’adin saboda shiryen shiryen zaben da ake yi a shekarar 2026.

An amince da kudurin da kuri’u 14 sai kuma kin amincewa daga Amurka.

An samar da tawagar ta MINUSCA a watan Afrilun 2014 don kokarin kawo karshen yakin basasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan Shugaba François Bozizé.

Rage kasafin kudin Amurka, ya tilasta wa Majalisar Dinkin Duniya rage yawan sojojinta da aka tura a duk duniya, wanda ya sanya kwamitin tsaro ya dan rage yawan sojojin MINUSCA zuwa (14,046 daga 14,400 a baya) tare da jaddada “aniyar sake duba adadin ma’aikatan bayan kammala nasarar aiwatar da zaben da aka tsara a 2025 da 2026.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments