Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza

 Hukumar Agaji mai kula da Falasdinu dake karkashin MDD, ( Unrwa)  da ta fitar da wannan alkaluman na yawan gidajen da ‘yan mamaya su ka

 Hukumar Agaji mai kula da Falasdinu dake karkashin MDD, ( Unrwa)  da ta fitar da wannan alkaluman na yawan gidajen da ‘yan mamaya su ka rushe, ta kuma kara da cewa; Da akwai dubban iyalai Falasdinawa da suke raywua a cikin hemomi kuma a cikin mawuyancin yanayi, ga shi kuma sanyi yana karatowa.

Hukumar ta Agaji ta kuma sanar da cewa; Ta dogara ne da bayanai da ake amfani da su wajen raba kayan agaji da kai tsaye MDD take da hannu a ciki tare da aikin hadin gwiwa da kungiyar “Red Corss” da kuma kungiyar “Red Crecent”.

Unrwa ta kuma ce; Tana aiki a tare da sauran kungiyoyin agaji wajen rabawa iyalan Falasdinawa kayan agaji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted