Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire

Kasar Cote De Voire ta sanar da tsaurara harkokin tsaro akan iyakokinta na Arewa domin fuskantar ‘yan hijira da suke kwararowa daga kasar Mali da

Kasar Cote De Voire ta sanar da tsaurara harkokin tsaro akan iyakokinta na Arewa domin fuskantar ‘yan hijira da suke kwararowa daga kasar Mali da take fama da rikicin masu dauke da makamai.

Majalisar tsaron kasar “Cote De Voire” ce ta bai wa sojojin kasar umarni da su tabbatar da tsaro a kan iyakoki, kamar yadda gwamanti ta bayyana.

A can cikin kasar Mali mai makwabtaka da “Cote De Voire” ana samun karuwar hare-haren masu dauke da makamai akan fararen hula da hakan yake kara yawan kwararan ‘yan hijira.

Mali wacce ba ta da iyaka ta ruwa tana fama da rikickin masu dauke da makamai dake da alaka da kungiyar alka’ida da su ka tsananta kai hare-hare daga  watan Satumbar da ya gabata.Masu dauke da makaman dai sun datse kan iyakar kasar da hana shigar da man fetur da hakan ya haddasa kamfar man fetur. An rufe gidajen mai masu yawa da kuma makarantu saboda babu ababen hawa da za su yi jigilar dalibai.

Kungiyar mai suna: “Nusratul-Islami Wal Muslimin” tana kara nausawa daga yammacin kasar zuwa kudu, da hakan yake jefa tsoron cewa za su kwace madafan iko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments