Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin

Ministan yakin Amurka  Pete Hegseth  ya bayyana cewa kasar tasa ta fara kai farmakin da ta kira ” Mashin Kudu” akan dillalan muggan kwayoyi. Ministan

Ministan yakin Amurka  Pete Hegseth  ya bayyana cewa kasar tasa ta fara kai farmakin da ta kira ” Mashin Kudu” akan dillalan muggan kwayoyi.

Ministan yakin na Amurka ya rubuta a Shafin X cewa; manufar wannan farmakin shi ne kare kasarmu, da kawo karshen masu dillancin muggan makamai ‘yan ta’adda, da kare kasarmu daga muggan kwayoyin da suke kashe mana ‘yan kasa.”

 Gwamnatin Donald Trump dai ta bude kai hare-hare akan jiragen ruwan a doron ruwan Carrebia da tekun Pacific bisa abinda take riya cewa masu fataucin muggan kwayoyi ne.

Sai dai har yanzu babu wani dalili guda daya da Amurkan ta gabatar da shi wanda yake nuni da cewa wadannan jiraegen ruwa da take kai wa harin suna dauke da muggan kwayoyi.

Amurka din ta girke jiragen ruwa na yaki da su ka hada da “Gerald Ford”.

Kafafen watsa labarun Amurka da su ka hada da ” CBS” sun ambaci cewa, makusantan Donald Trump sun ba shi shawarar kai hare-hare a cikin kasar Venezuela.

A nata gefen, gwamantin kasar ta Venezuela ta sanar da girke sojoji a fadin kasar domin fuskantar duk wani hari daga kasar Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments