Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya a yankin

Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data

Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya.

A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Ministocin Harkokin Wajen Iran da Turkiyya sun yi nazari kan dangantakar kasashen biyu kuma sun jaddada muhimmancin karfafawa da bunkasa dangantaka a dukkan fannoni masu amfani.

Yayin da yake yaba wa kokarin rage tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada muhimmancin karfafa shawarwari don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kuma ya bayyana anniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na bayar da tallafi a wannan fanni.

Araqchi ya kuma mika ta’aziyya ga Turkiyye sakamakon rasuwar wasu sojojinta a hatsarin jirgin saman sojan da ya faru kwanan nan.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyye, a nasa bangaren, ya jaddada a yayin wannan tattaunawar ta wayar tarho, cewa yana mai dogaro da duk wani yunkuri na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments