Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza

Rasha, China, da wasu kasashen Larabawa da dama sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yaki da kuma rashin wani muhimmin matsayi ga Hukumar

Rasha, China, da wasu kasashen Larabawa da dama sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yaki da kuma rashin wani muhimmin matsayi ga Hukumar Falasdinu bayan yakin Gaza da aka gabatar a daftarin kudirin shirin tsagaita wuta na Shugaba Donald Trump na Amurka.

Duk da cewa jami’an diflomasiyyar kasashen sun yarda cewa tattaunawa ta kai ga cimma yarjejeniyar, amma rarrabuwar kawuna tsakanin Washington da wasu membobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, bayan fiye da shekaru biyu na kisan kare dangi.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ya kamata a amince da kudurin nan take, yana mai jaddada bukatar gaggauta amincewa da shirin.

Daftarin farko na Amurka, wanda aka rarraba a makon da ya gabata, ya yi kira da a samar da babban mataki da zai bai wa rundunar kasa da kasa damar aiki a Gaza har zuwa 2027 tare da wata Hukumar Zaman Lafiya, wadda har yanzu ba a kafa ta ba.

Kasashen Larabawa wadanda suka nuna sha’awar bayar da gudummawar sojoji sun ce irin wannan izini yana da mahimmanci.

Rasha, China, da Aljeriya sun yi watsi da daftarin.

Mahimman abubuwan da ke kawo tarnaki ga shirin su ne rashin wata hanya bayyananna ga samar da kasar Falasdinu da rashin tabbas game da lokacin da sojojin Isra’ila za su janye daga Gaza.

Rasha ta gabatar da nata kudirin kan Gaza, tana kalubalantar kokarin Amurka na ganin Kwamitin Tsaro ya amince da shirin zaman lafiya na Shugaba Donald Trump kan Gaza, a cewar kwafin daftarin da Reuters ta samu gani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments