Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha

Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da ta sami rahotanni daga wasu daga cikin kasashen gabacin turai kan cewa […]

Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa

Yan sa’o’ii da janyewar sojojin HKI a wasu yankunan Gazaa aka fara gano gawakin Falasdinwa wadanda HKI ta kashe su a kan tituna da kuma karkashin burbushin gine-gine. Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza, ta bada danarwan gani gawakin shahidan Falasdinawa 17 a cikin dan karamin lokaci da janyewar sojojin yahudawa daga wasu yankuna  A Gaza. […]

Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza

Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa […]

Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran

Ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanya takunkumi kan wasu mutane sama da 50 da hukumomi da jiragen ruwa da ake zargi da hannu a cinikin man fetur da Iran. A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, ofishin kula da kadarorin kasashen waje (OFAC) ta kara matsin lamba kan Iran ta hanyar kakaba mata takunkumi ga […]

Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki

Yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza ta fara aiki da safiyar yau, kamar yadda rundunar sojin Isra’ila ta sanar. A cikin sa’o’i 72 ne ake sa ran sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a musayar fursunonin Falasdinu. Tunda farko dama gwamnatin Isra’ila ta sanarda amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Hamas, wadda […]

Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta  dindindin

Shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza kuma shugaban tawagar Falasdinawa Khalil al-Hayya ya sanar da cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki da cin zarafin al’ummar Palasdinu, da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin a zirin Gaza, gami da janye sojojin mamaya, shigar da kayan agaji, bude mashigar Rafah ta bangarori biyu, da musayar fursunoni. […]

Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran  a Yamai

Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Sahabi Oumarou, ya gana da  Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar. A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi alakoki da ke tsakanin kasashe biyu da kuma yadda za a kara inganta su. Sannan kuma sun yi musayar ra’ayi kan hadin gwiwa tsakanin […]

Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump ya gabatar

Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tsare tsare da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a hukumance, kamar yadda ofishin Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Juma’a. Wannan dai na zuwa ne bayan ci gaba da tsaikon da aka samu  na tsawon kwana daya biyo bayan […]

Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan  damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta […]