Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha

Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar.

Majalisar dokokin tarayyar Turai ta amince wa kasashen nahiyar su kakkabo jiragen yakin kasar Rasha wadanda suke keta sararin samaniyar wasu daga cikin kasashen Nahiyar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da ta sami rahotanni daga wasu daga cikin kasashen gabacin turai kan cewa jiragen yakin kasar Rasha samfurin Mig 31 da Su 25 keta sararin samaniyar kasashensu.

Firay ministan kasar Poland Donal Tusk ya ce kasarsa a shirye take ta kakkabo duk wani abu da ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.

A taron majalisar don tattauna wannan batun dai wakilai 469 sun amince da bukatar a yayinda wasu 97 suka ki amincewa, sai kuma 38 wadanda suka ki kada kuri’unsu.

Jiragen yakin kasar Rasha masu tsananin sauri sun keta sararin samaniyar kasashen Poland, Estonia, Latvia, Lithuania, da kuma Romania. Sannan jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar ta Rasha sun keta sararin samaniyar kasashen Denmark, Sweden, and Norway.

Labarin yace jiragen yakin Rasha samfurin MiG-31 guda uku sun keta sararin samaniyar kasar Estonia a ranar 19 gawatan satumban da ya gabata, sannan an gawa wani jirgin Rasha yana shawagi kan kamfanin manfetur da gasa mai suna ‘ Petrobaltic oil and gas platform a kasar  Poland ba tare da izini ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments