Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan  damar.

Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta ka’idojin yarjejeniyar, da kuma rungumar damar da tke cikinta.”

Duk da cewa dai a  cikin kalaman nasa yafi nuna damuwa a kan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, duk da irin mummunan kisan kiyashi da Isra’ila take yi a Gaza, amma mya ce Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsaf domin ba da cikakken goyon bayanta ga aiwatar da yarjejeniyar.

A halin da ake ciki kuma, ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a wanan  Alhamis ta ba da rahoton cewa, ‘yan  sa’o’i  bayan tattaunawar tsagaita bude wuta tsakanin kungiyar Hamas da “Isra’ila”, Isra’ula ta kaddamar da wasu hare-haren a Gaza inda ta kashe mutane goma sha daya.

Yayin da mazauna yankin ke jiran aiwatar da yarjejeniyar tare da dakatar da kai hare-haren bama-bamai, ofishin ya bukaci ‘yan kasar da su guji yin zirga-zirga a kan titunan al-Rashid da Salah al-Din ko kuma a yankunansu har sai an fito fili a fili.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana a  dandalin telegram cewa, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, asibitoci a zirin Gaza na ci gaba da karbar wadanda suka yi shahada, inda aka kashe mutane goma sha daya, daya daga cikinsu ya mutu a karkashin baraguzai da wasu arba’in da tara suka jikkata. Ma’aikatar ta kara da cewa an kuma kashe mutane biyu a cibiyoyin raba kayan agaji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments