Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta  dindindin

Shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza kuma shugaban tawagar Falasdinawa Khalil al-Hayya ya sanar da cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki da cin zarafin al’ummar Palasdinu,

Shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza kuma shugaban tawagar Falasdinawa Khalil al-Hayya ya sanar da cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki da cin zarafin al’ummar Palasdinu, da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin a zirin Gaza, gami da janye sojojin mamaya, shigar da kayan agaji, bude mashigar Rafah ta bangarori biyu, da musayar fursunoni.

Al-Hayya ya bayyana cewa kungiyar ta samu lamuni daga masu shiga tsakani da gwamnatin Amurka, yana mai jaddada cewa dukkan bangarorin sun jaddada cewa an kawo karshen yakin.

Ya bayyana cewa yarjejeniyar ta hada da sakin fursunoni 250 da ke zaman daurin rai-da-rai, fursunoni 1,700 daga zirin Gaza da Isra’ila ta  kama bayan 7 ga watan Oktoba, da kuma sakin dukkan yara da mata.

A cikin jawabin nasa, Al-Hayya ya ce, duniya ta tsaya tsayin daka kan sadaukarwa, dagewa, da hakurin da al’ummar zirin Gaza suke yi. Ya yi nuni da cewa al’ummar yankin sun yi juyiriya  da duniya ba ta taba ganin irinta ba, inda suka fuskanci zalunci,  da mummunan kisan kiyashi na makiya.

Ya kara da cewa al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka kamar tsaunuka, kudurinsu bai gushe ba wajen tinkarar kisa, kauracewa gidajensu, yunwa, da asarar dangi da gidaje. Ya jinjina wa shahidan da suka yi sadaukarwa baki daya, musamman  shugabanni Ismail Haniyeh, Saleh al-Arouri, Yahya Sinwar, da Mohammed Deif.

Al-Hayya ya bayyana godiyarsa da jinjina ga kasashe da dakarun da suka bayar da gudunmawa daga Yemen, Labanon, Iraki, zuwa  Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma ‘yantattun mutane a fadin duniya da suka tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya ga Gaza, musamman wadanda suka halarci ayarin tallafi da ‘yanci ta kasa da ruwa, da duk wanda ya ba da gudummawa wajen bayyana kalmar gaskiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments