Ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanya takunkumi kan wasu mutane sama da 50 da hukumomi da jiragen ruwa da ake zargi da hannu a cinikin man fetur da Iran.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, ofishin kula da kadarorin kasashen waje (OFAC) ta kara matsin lamba kan Iran ta hanyar kakaba mata takunkumi ga mutane sama da 50, kamfanoni da jiragen ruwa masu saukaka sayarwa da jigilar danyen mai da iskar gas daga Iran.
A cewar hukumomin Amurka, wadannan hanyoyin sun baiwa Iran damar fitar da mai da kayayyakin da suka kai na biliyoyin daloli.
Sabon takunkumin ya shafi kamfanoni uku da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, kamfanoni uku na bogi a Hong Kong, da wata matatar mai a China.
Wannan bas hi ne karon farko da Amurka ke kakaba takunkumi kan kamfanoni masu alaka da iran bisa zarginsu da cikin mai da iran, inda ko a farkon watan Oktoba, ofishin kula da kadarorin kasashen waje (OFAC) ya sanya takunkumi ga hukumomi 21 da wasu mutane 17 da ake zargi da taimakawa wajen sayo wasu kayayyaki na fasaha ga ma’aikatar tsaron Iran.