Mai Magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar Palastinu a gwagwarmayar neman ‘yanci da mutunci.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mohajerani ta ce Iran za ta goyi bayan duk wani mataki ko wani shiri da zai kai ga dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, da janyewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila, da shigar da kayayyakin jin kai, da sakin fursunonin Falasdinu, da kuma tabbatar da hakkinsu na yau da kullun.
Ta yi nuni da cewa goyon bayan Iran ga al’ummar Palasdinu “ba matsayi ne na siyasa kawai ba, a’a yana dogara ne akan imani da ‘yancin al’ummar Palasdinu da kuma tsayin daka wajen kin amincewa da zalunci da mamaya.” Ta nanata cewa tsayin dakan da al’ummar Palasdinu suke yi ya dace kuma yana wakiltar wani muhimmin bangare na tsarin maido da ‘yancin Falasdinu.
Mohajerani ta kara da cewa dakatar da laifuffukan da ake yi a Gaza “ba shi ne karshen lamarin ba, dole ne a bi kadun lamarin a gaban kotunan duniya domin hukunta wadanda suka yi umarni da aikata laifukan yaki, da kisan kare dangi, da cin zarafin bil’adama,” tana mai kira ga kasashen duniya da su dauki nauyin bin kadun wannan shari’a.
A baya ma dai ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da goyon bayan Tehran ga duk wani mataki ko wani shiri da ya hada da dakatar da yakin kisan kiyashi da ake yi wa Palastinawa, tare da bayyana bukatar dukkanin bangarorin da su yi taka tsantsan kan abin da ta bayyana a matsayin yaudara irin ta yahudawan sahyoniyawa da yadda suke keta yarjejeniyoyin kasa da kasa.