Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran  a Yamai

Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Sahabi Oumarou, ya gana da  Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar. A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna

Ministan albarkatun mai na Jamhuriyar Nijar Sahabi Oumarou, ya gana da  Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar.

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimamn batutuwa da suka shafi alakoki da ke tsakanin kasashe biyu da kuma yadda za a kara inganta su.

Sannan kuma sun yi musayar ra’ayi kan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fuskar cin moriyar juna.

Jamhriyar Nijar da Iran suna da kyakkawar alaka  ta diflomasiyya, kamar yadda kuma suna yarjeniyoyi da dama da ayyukan hadin gwiwa a fagage daban-daban na diflomasiyya, cinikayya da bunkasa harkoki tattalin arziki da kimiyya da fasaha.

Bangarorin biyu sun jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna domin aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyi da aka rattaba hannu a kansu a tsakanin kasashen biyu a dukanin bangarori, musamman ta fuskar harkokin makamashi da cinikayya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments