Yan sa’o’ii da janyewar sojojin HKI a wasu yankunan Gazaa aka fara gano gawakin Falasdinwa wadanda HKI ta kashe su a kan tituna da kuma karkashin burbushin gine-gine.
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza, ta bada danarwan gani gawakin shahidan Falasdinawa 17 a cikin dan karamin lokaci da janyewar sojojin yahudawa daga wasu yankuna A Gaza.
Ma’aikatar ta ce an kawo gawaki 17 da wasu 71 da suka ji rauni, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata.
Zuwa yau jumma’a ma’aikatar ta bayyana cewa yawan mutanen da HKI ta kashe a gaza sun kai 67,211 da wasu 169,961 na wadanda suka ji rauni daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.
Labarin ya kara da cewa masu neman tallafin abinci wadanda sojojin yahudawan da kuma MAurka suka kashe sun kai mutum 2,615 sannan wasu 19,182 kuma suka ji rauni.
Ma’aikatar ta kara da cewa akwai gawaki da dama a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa.